ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa fadan ya tashi ne a lokacinda sojojin kasar suka nufi gadin tsohon spetan ‘yansandan a birnin Magadishu, wanda hakan ya raba kan jami’an tsaron kasar suka kuma fara kaiwa juna hare-hare. Shugaba Muhammad Farmajo yak i amincewa ya tsawaita wa’adin shugugab ‘yansandan kamar yadda ya bukata.
Tuni dai gamayyar jam’iyyun adawar kasar ta Somalia sun bayyana cewa zasu kama gwamnatin bayen fage bayan da majalisar dokokin kasar ta amince da tsawaitawa Farmajo gwamnatinsa na shekaru biyu.
Tun shekara ta 1991 ne kasar Somalia ta fada cikin rikicin kabilanci wanda ya kaida kungiyar Alshabab wacce take kawance da kungiyar alka’ida da mamaye mafi yawan kasar a wani lokaci. Sai dai duk tare da shigar sojojin nahiyar Afirka cikin rikicin har yanzu kasar bata sami zaman lafiya ba.
342/